Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta ce ta ƙara zage damtse wajen ceto Shugaban Ƙaramar Hukumar Bunguɗu ta Jihar Zamfara, Hon. Nura Umar Abdullahi, bayan da wasu ’yan ta’adda suka yi garkuwa da shi a safiyar Asabar.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labaran Rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya fitar, ya bayyana cewa maharan sun kai hari gidan shugaban ƙaramar hukumar a cikin dare, inda suka yi galaba kan jami’an ’yan sanda da masu sintiri da ke ba shi kariya kafin su yi awon gaba da shi tare da wasu daga cikin iyalansa
- An sace Shugaban Ƙaramar Hukuma a Zamfara, an kashe jami’an tsaro huɗu
- Akwai bukatar ƙasashen Afirka su yi amfani da albarkatun ƙasarsu don samun matsayi a kasuwannin duniya – Shettima
- Ba mu bada umurnin harbe duk wanda aka gani ɗauke da bindiga ba – ‘Yan sanda
Sai dai sanarwar ta ce da jin ƙarar harbe-harbe, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun isa wurin cikin gaggawa tare da bin sawun maharan, lamarin da ya haifar da musayar wuta mai tsanani
A cewar rundunar, matakin gaggawar da dakarun suka ɗauka ya tilasta wa ’yan ta’addan sakin mutum biyar daga cikin iyalan shugaban ƙaramar hukumar. Waɗanda aka ceto sun haɗa da ’ya’yansa biyu da mahaifiyarsa da matarsa da wani ɗan uwansa.
Idan dai za a iya tunawa a daren Alhamis ne wasu ’yan bindiga suka afka gidan shugaban ƙaramar hukumar inda suka sace shi.