Tawagar mata ta Najeriya a wasan mutum uku-uku na wasan kwando na kujera ta sha babban kaye da ci 16-1 a hannun Scotland a wasansu na farko a gasar ƙasashe rainon Ingila ta 2026.

Scotland ta mamaye wasan daga farko har zuwa ƙarshe, inda ta bar ‘yan Najeriya da rashin yin tasiri a wasan.

Nofisat Adefala ce ta ci wa Najeriya maki ɗaya tilo a wasan, yayin da ‘yan Scotland din suka nuna ƙwazonsu wajen kai hare-hare da tsaron gida don samun nasara mai ƙayatarwa.

Wannan shan kaye ya sa Najeriya za ta ƙara ƙaimi domin gyara kura-kuren da aka samu domin tunƙarar wasaani na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *