Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta sanar da kama hodar iblis (cocaine) da Loud da magungunan opioids da darajarsu ta haura Naira biliyan 10 a tashoshin jiragen ruwa da na sama da ke Legas, tare da cafke wasu da ake zargin manyan jagororin safarar miyagun kwayoyi ne.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce jami’anta sun kama wani dan kasuwa mai shekara 55, Onuigbo Ndubisi Chinedu, wanda ke sana’ar sayar da kayan sawa a kasuwar Balogun da ke Legas Island, bisa zargin yunkurin fitar da kilogram 3.30 na hodar iblis zuwa Birtaniya.

An ce an boye hodar iblisin ne a cikin bangon kwalayen da aka shirya kayan abinci a ciki.

Jami’an NDLEA sun kama shi ne ranar 23 ga Yuli, 2026, bayan sun tare kayan da ake son fitarwa a filin jirgin saman Legas.

Binciken da aka gudanar ya kai ga cafke jami’an jigilar kaya uku da wani mutum mai suna Kenneth Okakpu, wanda ya kai kayan domin a tura su zuwa Birtaniya. Daga bisani ne binciken ya gano cewa Onuigbo ne jagoran kungiyar masu safarar miyagun kwayoyin.

A wani samame kuma, hukumar ta ce ta kwace kwayoyi 2,240,000 na maganin Tapentadol 250mg, wadanda darajarsu ta haura Naira biliyan 2.2.

An shigo da su ne daga Indiya cikin jirgin Air Maroc, kuma an gano su ne bayan samun sahihan bayanan sirri.

A tashar jiragen ruwa ta Apapa kuwa, jami’an NDLEA sun gano wata kwantena dake dauke da motoci uku da aka yi amfani da su wajen boye buhuna 4,777 na Canadian Loud masu nauyin kilogram 2,388.5, wadanda darajarsu ta haura Naira biliyan 7.1.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *