Kwamitin Majalisar Wakilai da ke binciken hukumar bogi PFIPC ya umarci Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Disu, da ya gabatar da mutumin da ke ikirarin cewa shi ne Darakta Janar na hukumar, Adeyemi Adeniyi, a gaban kwamitin ranar Laraba.

An bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin yayin da aka ci gaba da zaman binciken da ake gudanarwa a harabar Majalisar Tarayya da ke Abuja.

Umarnin ya biyo bayan tabbatarwar da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta yi game da wasu muhimman sassan bincikenta na laifuka, ciki har da koke-koken da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa ya shigar, wanda ke zargin Adeyemi da gabatar da kansa ta hanyar yaudara a matsayin Darakta Janar na Kwamitin Tattalin Arzikin Shugaban Ƙasa (Presidential Economic Advisory Council) da kuma Kwamitin Shugaban Ƙasa na Bunƙasa Zuba Jarin Ƙasashen Waje (PFIPC).

Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, ya ce wajibi ne Adeyemi ya bayyana a gabansu saboda girman zarge-zargen da ake masa da kuma manyan hukumomin gwamnati da lamarin ya shafa.

Tun da farko, ACP Bashir Abdullahi ya shaida wa ’yan majalisar cewa, duk da cewa bincike na ci gaba, rundunar ’yan sanda ta riga ta shigar da ƙara mai tuhuma takwas a kan Adeyemi a gaban Babbar Kotun Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *