Hukumar Tsara Jarabawar Larabci da Darussan Islama ta Ƙasa (NBAIS) ta ware kimanin naira biliyan 18.049 domin biyan albashi da sauran haƙƙoƙin ma’aikatanta a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.
Kasafin kuɗin hukumar na shekarar 2026 ya kai naira biliyan 26.47, wanda ke nuna cewa kusan kashi 68 cikin 100 na jimillar kuɗin da aka ware wa hukumar za su tafi ne wajen biyan ma’aikata.
Bayanan kasafin sun nuna cewa an ware naira miliyan 146.6 domin alawus-alawus, yayin da aka tanadi naira biliyan 2.49 domin gudunmawar walwala ta ma’aikata.
- Gwamnatin Tarayya ta baiwa tawagar ‘yan wasan ɗaga nauyi na masu buƙata ta musamman kyautar kuɗaɗe
-
INEC ta sanar da rufe aikin rijistar katin zaɓe a yau Lahadi
Daga cikin kuɗin gudunmawar walwalar, an ware naira miliyan 770.1 domin Asusun Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS) da naira biliyan 1.54 a matsayin gudunmawar gwamnati ga fansho, sannan naira miliyan 178.7 domin Asusun Diyyar Ma’aikata (Employees’ Compensation Scheme).
Sauran kashi 32 cikin 100 na kasafin za su haɗa da naira miliyan 318 domin gudanar da ayyukan yau da kullum, yayin da aka ware naira biliyan 8.1 domin ayyukan raya ƙasa.
Kasafin ya kuma tanadi sama da naira biliyan 2.5 domin ayyuka da suka haɗa da gina hanyoyi, da girke fitilun tituna masu amfani da hasken rana, da rabon kayan tallafi da kuma horas da matasa kan amfani da kafafen sada zumunta. Waɗannan ayyuka sun fi mayar da hankali ne a jihohin Kano, Katsina, Kogi da Zamfara.
Daga cikin ayyukan da aka ware wa kuɗi akwai naira miliyan 210 domin gina titin Dantata zuwa Saint Louis a Kano ta Tsakiya, da kuma naira miliyan 70 domin gina titin kilomita 1.5 a Ugwolawo da ke ƙaramar hukumar Ofu a jihar Kogi.
Hukumar ta kuma ware naira miliyan 84 domin kammala wasu masana’antu a Kogi ta Gabas, tare da naira miliyan 70 domin kammala ginin ofishin rundunar NSCDC a yankin Sharada na Kano.
A jihar Zamfara kuwa, an ware naira miliyan 28 domin rabon shinkafar tuwo ga al’ummomin mazabar Anka/Talata Mafara, yayin da aka ware naira miliyan 70 domin tallafa wa mazauna mazabar Danbatta/Makoda ta Kano da kayan sana’a da kuɗaɗe.
Babban kaso daga cikin ayyukan raya ƙasar ya tafi ne wajen girke fitilun tituna masu amfani da hasken rana a ƙananan hukumomi da dama na Kano ta Tsakiya, inda jimillar kuɗin da aka ware wa wannan aiki ta haura naira biliyan 1.5.
Hukumar NBAIS Ta Kashe Naira Biliyan 18 Kan Albashin Ma’aikata a Kasafin Kuɗin 2026
Hukumar Kula da Jarabawar Larabci da Addinin Musulunci ta Ƙasa (NBAIS) ta ware kimanin naira biliyan 18.049 domin biyan albashi da sauran haƙƙoƙin ma’aikatanta a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.
Kasafin kuɗin hukumar na shekarar 2026 ya kai naira biliyan 26.47, wanda ke nuna cewa kusan kashi 68 cikin 100 na jimillar kuɗin da aka ware wa hukumar za su tafi ne wajen biyan ma’aikata.
Bayanan kasafin sun nuna cewa an ware naira miliyan 146.6 domin alawus-alawus, yayin da aka tanadi naira biliyan 2.49 domin gudunmawar walwala ta ma’aikata.
Daga cikin kuɗin gudunmawar walwalar, an ware naira miliyan 770.1 domin Asusun Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS) da naira biliyan 1.54 a matsayin gudunmawar gwamnati ga fansho, sannan naira miliyan 178.7 domin Asusun Diyyar Ma’aikata (Employees’ Compensation Scheme).
Sauran kashi 32 cikin 100 na kasafin za su haɗa da naira miliyan 318 domin gudanar da ayyukan yau da kullum, yayin da aka ware naira biliyan 8.1 domin ayyukan raya ƙasa.
Kasafin ya kuma tanadi sama da naira biliyan 2.5 domin ayyuka da suka haɗa da gina hanyoyi, da girke fitilun tituna masu amfani da hasken rana, da rabon kayan tallafi da kuma horas da matasa kan amfani da kafafen sada zumunta. Waɗannan ayyuka sun fi mayar da hankali ne a jihohin Kano, Katsina, Kogi da Zamfara.
Daga cikin ayyukan da aka ware wa kuɗi akwai naira miliyan 210 domin gina titin Dantata zuwa Saint Louis a Kano ta Tsakiya, da kuma naira miliyan 70 domin gina titin kilomita 1.5 a Ugwolawo da ke ƙaramar hukumar Ofu a jihar Kogi.
Hukumar ta kuma ware naira miliyan 84 domin kammala wasu masana’antu a Kogi ta Gabas, tare da naira miliyan 70 domin kammala ginin ofishin rundunar NSCDC a yankin Sharada na Kano.
A jihar Zamfara kuwa, an ware naira miliyan 28 domin rabon shinkafar tuwo ga al’ummomin mazabar Anka/Talata Mafara, yayin da aka ware naira miliyan 70 domin tallafa wa mazauna mazabar Danbatta/Makoda ta Kano da kayan sana’a da kuɗaɗe.
Babban kaso daga cikin ayyukan raya ƙasar ya tafi ne wajen girke fitilun tituna masu amfani da hasken rana a ƙananan hukumomi da dama na Kano ta Tsakiya, inda jimillar kuɗin da aka ware wa wannan aiki ta haura naira biliyan 1.5.
Kasafin ya kuma ƙunshi naira miliyan 75.6 domin horas da matasa kan kafafen sada zumunta da na zamani, tare da naira miliyan 49 domin horas da matasa da mata yadda za su mayar da robobi da aka zubar zuwa tayal na shimfiɗa a mazabar Dutsin-Ma/Kurfi ta jihar Katsina.
Jaridar Daily Trust ta ce ƙoƙarin jin ta bakin jami’an hukumar bai yi nasara ba a lokacin da wakilinta ya ziyarci hedikwatar hukumar da ke kan titin Kaduna zuwa Zariya. Sai dai shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar, Abdul Salam Ramalan, ya ce zai mayar da martani bayan ya tuntubi shugabanninsa. Wata majiya daga cikin hukumar ta ce yawancin ma’aikatan suna sa ido ne kan jarabawar watan Yuni zuwa Yuli, tare da bayyana cewa hukumar na da kusan ma’aikata 6,000.
Wasu masana sun soki yadda ake tafiyar da hukumar. Daraktan Cibiyar Bincike Kan Gaskiya da Riƙon Amanar Kuɗaɗen Jama’a, Dakta Umar Yakubu, ya ce ya kamata a soke NBAIS, yana mai cewa ayyukanta za su iya komawa hukumomi irin su WAEC ko JAMB domin kauce wa maimaita ayyuka da kuma rage almubazzaranci da kuɗaɗen gwamnati.
Rahoton ya kuma tuna cewa tun bayan amincewar Hukumar Ilimi ta Ƙasa (NCE) a shekarar 2011 da NBAIS a matsayin hukumar gudanar da jarabawa ta ƙasa, an ɗauki sama da ma’aikata 5,000. Sai dai wasu ma’aikatan da suka yi magana ba tare da an bayyana sunayensu ba sun ce da dama daga cikinsu ba su da takamaiman aikin yi ko jadawalin aiki, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce kan yadda ake gudanar da hukumar.Hukumar NBAIS Ta Kashe Naira Biliyan 18 Kan Albashin Ma’aikata a Kasafin Kuɗin 2026

Rahoton ya kuma tuna cewa tun bayan amincewar Hukumar Ilimi ta Ƙasa (NCE) a shekarar 2011 da NBAIS a matsayin hukumar gudanar da jarabawa ta ƙasa, an ɗauki sama da ma’aikata 5,000. Sai dai wasu ma’aikatan da suka yi magana ba tare da an bayyana sunayensu ba sun ce da dama daga cikinsu ba su da takamaiman aikin yi ko jadawalin aiki, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce kan yadda ake gudanar da hukumar.