Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yanke wa wani shugaban safarar miyagun ƙwayoyi, Ntoruka Emmanuel Chinedu, da tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasa da ƙasa, Hunkarin Segun George, hukuncin ɗaurin shekaru 24 a gidan yari bisa shigo da hodar iblis Najeriya ba bisa ƙa’ida ba.
Kotun, ƙarƙashin Mai Shari’a Musa Kakaki, ta yanke wa Chinedu hukuncin shekaru 22 a gidan yari, unkarin shekaru biyu, bayan an same su da laifin shigo da kilogram 7.05 na hodar iblis.
NDLEA ta ce an fara gurfanar da Chinedu tun shekarar 2015 kan shigo da kilogram 6.25 na hodar iblis, amma ya tsere bayan an ba shi beli, inda ya shafe kusan shekaru goma yana gudun hijira.
- Ranar hana mutuwa a ruwa ta duniya: An karrama masu ceto a ruwa
- NDLEA ta kama miyagun kwayoyi na sama da naira biliyan 10, ta cafke manyan masu safarar su
Sai dai a watan Yunin 2025 jami’an NDLEA suka sake cafke shi a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas yayin da yake ƙoƙarin shigo da gram 800 na hodar iblis daga Addis Ababa ta jirgin Ethiopian Airlines.
Bincike ya nuna cewa tsohon ɗan wasan ƙwallon, Hunkarin Segun George, na jiransa a filin ajiye motoci domin karɓar kayan, lamarin da ya kai ga cafke shi.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya yabawa hukuncin kotun, yana mai cewa ya nuna babu wani mai safarar miyagun ƙwayoyi da zai tsere daga hukunci, ko da ya ɗauki shekaru yana ɓuya.