‘Yan wasan kasa da shekaru 20 na Najeriya, Flying Eagles, sun fara yakin neman lashe gasar WAFU B U20 na bana da nasara mai kayatarwa inda suka doke Black Satellites na Ghana da ci 4-2 a ranar Litinin a kasar Ivory Coast.
Wannan sakamako ya bai wa Najeriya maki 3 da kuma zama a matsayi na daya a rukuni na B a kokarin su na fatan yin nisa a gasar yankin.
Olayemi Ayinla ne ya fara ci wa Najeriya kwallo ta farko a minti na 6. Amma Ghana ta farke kwallon da wuri a minit na 23 ta hannun Mohammed Zaidan, inda ta daidaita wasan da ci 1-1.
- Tawagun maza da mata na Najeriya sun samu tikitin shiga Gasar Ƙwallon Kwando ta ƙasashen Afirka ta 2026
- Anthony Joshua ya tuna da abokansa da suka rasu a Najeriya bayan ya doke Kristian Prenga
- Gasar Ƙasashe Rainon Ingila ta 2026: Scotland ta doke Najeriya a wasan Kwando na Kujera
Flying Eagles ta sake kasancewa kan gaba yayin da Lucky Oraro ya zura kwallo a raga, inda ci ya koma 2-1.
Sa’an nan a karshen rabi na farko, Najeriya ta samu bugun fanareti a minit na 38, inda Muiz Adeleke ya zura kwallon cikin nutsuwa, yayin da aka tafi hutun rabin lokaci ana ci 3-1.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, an bai wa Ghana bugun fanareti a minit na 60, inda Kelvin Nkrumah ya zura a raga kuma cin ya canza zuwa 3-2.
Najeriya ta sake samun wani bugun fenareti da ya cancanta a minti na 89, inda Adeleke ya zura kwallon sa ta biyu a wasan kuma aka kammala wasan ci 4-2.
A halin yanzu, Najeriya za ta nemi ta ci gaba da irin wannan kwazo a wasan su na gaba na rukuni da Togo ranar Laraba.