Tawagar Super Falcons ta Najeriya, za ta fara kare kambunta a Gasar Cin Kofin Ƙwallon Ƙafa ta Mata na Nahiyar Afirka (WAFCON) ta 2026, a ranar Talata da fuskantar Malawi a Rabat, Moroko.

Najeriya ce take riƙe da kofin a yanzu, wanda ta dauka bayan ta doke Moroko – mai masaukin baƙi – da ci 3-2 a wasan ƙarshe a 2024.

Ga muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da wannan wasa:

Super Falcons ta lashe Gasar WAFCON sau 10, kuma ita ce take riƙe da kofin a yanzu, yayin da Malawi take halarta a karo na farko a tarihi.

Tarihin haɗuwar ƙasashen biyu:

Najeriya da Malawi sun haɗu sau biyu a tarihi a matakin ƙasa-da-ƙasa na neman tikitin shiga Gasar Cin Kofin Mata ta Nahiyar Afirka a 2014.

A wasan farko sun tashi 1-1 a Blantyre, sannan daga baya Super Falcons ta yi nasarar doke su da ci 2-0 a wasan zagaye na biyu da suka buga a Abuja.

Manyan ’yan wasan da ake sa ran za su dauki hankali a fafatawar:

Najeriya: Kyaftin ɗin Super Falcons, Rasheedat Ajibade; mai tsaron raga, Chiamaka Nnadozie; da kuma shahararriyar ’yar wasan gaba, Asisat Osoala.

Malawi: ’yan wasan gaba, Temwa Chawinga da ’yar uwar ta, Tabitha Chawinga.

Za a take wasan ne da misalin karfe 9:00 na dare agogon Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *