Daya daga cikin manyan abubuwan al’ajabi a tarihin Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa ta Mata a Afirka (WAFCON) ya faru ranar Talata da dare.
A wasansu na farko a Rukunin C na bana, ‘yan basan The Scorchers (wadanda ake yiwa wannan lakabi saboda zafin namansu) na kasar Malawi sun kidima masu rike da kambun Gasar, wato Super Falcons na Najeriya da ci 3-2.
Wannan ne dai karo na farko da tawagar The Scorchers din ta fara siga Gasar, yayin da Super Falcons ta daga kofi har sau goma.
Wasan ya gudana ne a filin wasa na Al Madina da ke Morocco.
- Gasar WAFU B U20: Flying Eagles ta doke Black Satellites na Ghana da ci 4-2
- Tawagun maza da mata na Najeriya sun samu tikitin shiga Gasar Ƙwallon Kwando ta ƙasashen Afirka ta 2026
- Anthony Joshua ya tuna da abokansa da suka rasu a Najeriya bayan ya doke Kristian Prenga
‘Yar wasan gaba ta Malawi, Temwa Chawinga ce ta fi nuna bajinta, inda ta zura kwallaye biyu masu kayatarwa da suka taimaka wajen murkushe Super Falcons ta kuma tabbatar da nasara ta farko a tarihin WAFCON ga tawagar Scorchers.
A minti na 73 Temwa ta ci wallon farko da taimakon Ireen Khumalo.
‘Yar uwar Temwa din kuma, Tabitha Chawinga, ta ci kwallo ta biyu minti shida bayan nan.
Daga bisani Super Falcons din suka yunkura suka jefa kwallo daya ta kafar Rasheedat Ajibade wacce ta ci bugun fanareti a minti na biyu na karin lokaci.
Sannan Uchenna Kanu ta ci wa Super Falcons kwallo ta biyu a minti na tara na karin lokaci.
Wannan ne dai karo na farko da Super Falcons din ta sha Akashi a hannun wata tawaga da ta shiga Gasar a karo na farko.
Idan ba a manta ba, Malawi ce ta 153 a jerin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) na kasashen da suka fi fice a harkar kwallon mata, yayin da Najeriya take matsayin na 36.
Tawagar ta Malawi ce dai ta lasse Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa ta Mata ta Kudancin Afrika a 2023.
A yunkurinsu na samun garbi a Gasar ne ‘yan tawagar The Scorchers suka ci kwallaye mari yawa a tarihinta, inda ta yi wa Seychelles wankin babban bargo da ci 17 – 0.
A lokacin hazaka da kwazon ‘yan matan na Malawi, musamman Temwa da Tabitha (wadanda suka ci kwallaye da dama) suka bayyana.
Wannan shan kaye mai girgiza zuciya ya haddasa matsin lamba nan take a kan Super Falcons game da burinsu na lashe kofin a karo na 11 da kuma samun tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ta 2027 kai-tsaye.
A halin yanzu, Zambia ce ke jagorantar rukunin na C bisa bambancin kwallaye bayan ta yi wa Masar wankin babban bargo da ci 6-0 a wasan da suka buga da rana.
A halin yanzu dai dole ne Najeriya, wadda ba ta da maki ko daya, ta sake kyakkyawan shiri kafin ta fafata da Zambia a ranar 1 ga watan Agusta.
Malawi kuma za ta yi kokarin ci gaba da wannan nasara ta ban mamaki a wasanta na biyu da Masar.
