Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta musanta rahotannin da ake yadawa cewar a yankin ta aka kai hari kan wani jami’in soja, Kanal Abdussalam A. Ude.
Rundunar ta bayyana cewa lamarin bai faru a cikin yankin Babban Birnin Tarayya ba, sabanin yadda wasu kafafen yaɗa labarai da shafukan intanet suka ruwaito
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar a ranar Talata, ta ce bayan bincike da Kwamishinan ‘Yan Sandan, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya bayar da umarni, an gano cewa harin ya faru ne a Badna da ke Ƙaramar Hukumar New Karu ta Jihar Nasarawa.
- Gwamnati ta rufe makarantu a ƙananan hukumomi 20 dake jihar sokoto
- Tinubu zai sake ƙarawa sojoji albashi- Christopher Musa
- Masana sun bukaci a soke Hukumar Tsara Jarrrabawar Larabci da Darussan Islama ta kasa (NBAIS).
Rundunar ta ce wasu kafafen yada labarai sun danganta lamarin da Babban Birnin Tarayya ba tare da cikakken bayani ba, lamarin da ka iya jawo fargaba da rudani tsakanin mazauna babban birnin ƙasar
Kwamishinan ‘Yan Sandan FCT ya kuma bayar da umarnin tura jami’an tsaro domin tattara bayanan sirri zuwa yankunan da ke iyaka da Jihar Nasarawa, domin dakile duk wani yunkurin aikata laifuka shigowa cikin Abuja.
Rundunar ta yi kira ga kafafen yada labarai, masu rubuce-rubuce a yanar gizo da masu amfani da kafafen sada zumunta da su tabbatar da sahihancin bayanan tsaro daga hukumomin da abin ya shafa kafin wallafa su.
Ta kuma bukaci mazauna Abuja da su ci gaba da bin doka, tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta layukan gaggawa na rundunar.