Dan kwallon Brazil wanda ya fi kowa yawan zura kwallo a tarihin Kasar, Neymar, ya tabbatar da yin ritaya daga wasan kwallon kafa na kasa da kasa.

Neymar ya share kusan sama da shekaru 16 ya na buga wa Brazil wasa.

Brazil, ita ce kasa daya tilo da ta lashe Gasar cin Kofin Duniya sau biyar a tarihi.

Neymar, mai shekaru 34 ya sanar da hakan ne bayan ya taimaka wa kungiyar su ta Santos samun nasara da ci 4-2 a kan Universidad Central na kasar Venezuela a Gasar Copa Sudamericana.

Wannan ya kawo karshen hasashen da aka yi tsawon makonni kan makomarsa bayan ficewar Brazil daga Gasar cin Kofin Duniya ta 2026.

Tafiyar Brazil ta kare ne a zagaye na 16 bayan sun sha kashi ci 1-2 a hannun Norway, wasan da ya zama na karshe da Neymar ya buga wa kasar sa.

Da yake zantawa da manema labaru bayan samun nasarar Santos, Neymar ya bayyana cewa ba ya son ya sake wakiltar Brazil a wani wasa.

“Lokaci na tare da tawagar kasa ya kare. Na kafa tarihi, ina farin ciki sosai, na sadaukar da jinina, rayuwata, na yi gwagwarmaya kullum don ci gaban rigar mu, amma yanzu ba na son na sake maimaita hakan,” in ji Neymar.

Neymar ya yi murabus daga tawagar Brazil a matsayin dan kwallon da ya fi zura kwallo a tarihin kasar, inda ya kammala rayuwarsa ta kasa da kasa da kwallaye 80 da kuma bayar da taimakon zura kwallaye 59 cikin wasanni 130 da ya buga.

Kwallon da ya ci ta karshe ta kasa da kasa ta zo ne daga bugun fenareti a karin lokaci a kan Norway, a Gasar cin Kofin Duniya ta 2026 da aka kammala kwanan nan.

Neymar ya kuma taimaka wa Brazil lashe gasar FIFA Confederations Cup ta 2013, kuma ya jagoranci kasar zuwa lashe lambar Zinare a Gasar Olympics a wasannin Rio 2016, inda ya tabbatar da matsayinsa a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan kwallon kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *