Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta samu ƙarin tallafi a fannin tsaro, bayan wani mai hannu da shuni ya bai wa rundunar sabbin motocin sintiri guda biyu domin ƙara inganta ayyukan tsaro a yankin Bida.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, CP Adamu Abdullahi Elleman, ya bayyana cewa wannan tallafi zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan jami’an tsaro da kuma bunƙasa harkokin sintiri a yankunan da abin ya shafa.

Ya yabawa mai bayar da tallafin bisa wannan mataki, inda ya ce haɗin gwiwar jama’a da hukumomin tsaro na da muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kwamishinan ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan hali na tallafawa hukumomin tsaro, musamman a wannan lokaci da ake buƙatar haɗin kai wajen magance matsalolin tsaro.

Ya ƙara da cewa, duk da ƙoƙarin gwamnati wajen samar da kayan aiki ga hukumomin tsaro, yawan nauyin da ke kanta na iya hana ta biyan dukkan buƙatun al’umma cikin lokaci guda ba, don haka irin wannan haɗin gwiwa yana da muhimmanci wajen samun ingantaccen tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *