Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta samu nasarar ceto wani yaro mai suna Ubaiyu Muhammad Sammani, mai shekaru 9, da aka yi garkuwa da shi a unguwar R0be da ke Kano, ba tare da wani rauni ba.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane sun kama mutane 10 da ake zargi da hannu a cikin lamarin, ciki har da maza 9 da mace guda, bayan gudanar da bincike mai zurfi da amfani da bayanan sirri.

Rundunar ta ce an kai rahoton sace yaron ne ranar 9 ga Yuli, 2026, bayan mahaifinsa ya sanar da cewa wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun sace ɗansa tun ranar 6 ga Yuli, inda daga bisani suka nemi kuɗin fansa na dala 30,000.

Bayan fara bincike, jami’an ‘yan sanda sun gano wasu da ake zargi da taimakawa wajen aikata laifin, ciki har da waɗanda ake zargin sun taimaka wajen ɓoye yaron, sadarwa da masu neman kuɗin fansa, da kuma sauya wuraren da aka tsare shi.

Rundunar ta ce babban wanda ake zargi da shirya satar, Abubakar Salihu wanda aka fi sani da Sankolo, mai shekaru 25, yana gudu, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin cafke shi.

An ceto yaron ne ranar 31 ga Yuli, 2026, da misalin ƙarfe 8:30 na safe a yankin Karshen Kwata, Rimin Kebbe, inda aka kai shi asibiti don duba lafiyarsa, kuma an tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya.

Kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da aikata laifukan tashin hankali a jihar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *