Babbar Alkalin Najeriya (CJN), Justice Kudirat Kekere-Ekun, ta haramta yin amfani da kalmar ‘Barrister’ a matsayin lakabi kafin sunan lauya a dukkan harkokin hukuma na Kotun Koli ta kasa.
Wannan umarni ya fito ne ta hanyar wata sanarwa da babban magatakardan Kotun Koli, Kabir Akanbi, ya sanya wa hannu.
- Yan sanda sun dakile harin ‘yan bindiga jihar sokoto
- ABU da NAHCON sun sanya hannu kan fara digiri a fannin gudanar da aikin Hajji
- ‘Yan sanda sun ceto yaro ɗan shekara 9 da aka sace a Kano
Sanarwar ta shaida wa dukkanin jami’a a bangaren shari’a ciki har da lauyoyi, cewa yin amfani da taken Barristwr ya saba wa ka’idojin Koli.
Sai sanarwar ta bukaci wadanda abin ya shafa da su dakatar da yin amfani da lakabin a dukkanin rubuce-rubucen su ba tare da bata lokaci ba.
Har ila yau, sanarwar ta umarci shugabannin sashe a Kotun Koli. Da su tabbatar da an ni wan̈an umurnin.