Akalla sojoji sama da 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani harin da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai da sanyin safiyar Juma’a a kusa da garin N’guigmi da ke Jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun fara kai farmaki kan wani sansanin jami’an tsaron Garde Nationale kafin daga bisani ayarin sojojin da ya bi sawunsu ya fada cikin kwanton bauna a wani yanki da ke kusa da Tafkin Chadi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijar (ANP) ya ruwaito cewa Gwamnan Jihar Diffa, Janar Ibrahim Bagadoma, ya halarci jana’izar jami’an tsaron da suka mutu.

Yayin jana’izar, gwamnan ya isar da sakon ta’aziyyar Shugaban Kasar Nijar, Janar.

Abdourahamane Tchiani, da gwamnatin kasar ga iyalan mamatan, tare da jajanta musu kan wannan babban rashi.

Harin na zuwa ne yayin da hukumomin tsaron Nijar ke ci gaba da fuskantar barazanar hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai a yankin Tafkin Chadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *