Tawagar Najeriya ta kammala Gasar Kasashe Renon Ingila da ta halarta wanda aka gudanar a Glasgow ta 2026, a matsayi na shida a jerin teburin lambobin yabo da aka lashe gaba daya.
Najeriya ta lashe lambobin yabo 24 wadanda suka hada da zinare 10 da azurfa 7 da kuma tagulla 7.
Duk da wannan gagarumin nasarar, Najeriya ba ta cimma burin da Hukumar Wasanni ta Kasa (NSC) ta sa gaba kafin fara wannan gasar ba.
-
Zaben NFF: Za a fara sayar da fom ranar Asabar 1 ga Agusta
- WAFCON 2026: Yadda Algeria da Kenya suka sha kaye a hannun Moroko da Senegal
- WAFU B U20: Flying Eagles sun lallasa Sparrow Hawks da ci 3-0
Ko da yake kasar ta samu wasu manyan nasarori na tarihi a fannoni daban-daban na wasanni, adadin lambobin da aka samu ya yi kasa da abin da ake sa ran a hukumance da kuma nasarar da Najeriya ta samu da karya tarihi a Gasar Kasashe Renon Ingila ta 2022 da aka yi a Birmingham.
Kafin fara gasar, Darakta Janar na NSC, Bukola Olopade, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Tawagar Najeriya za ta iya lashe zinare fiye da 15 da aka kafa a karkashin shirin _Elite Athletes Podium Finish_ kuma za ta iya kai har zinare 22.

An gina wannan kyakkyawan fata ne kan sauye-sauyen tsari da Shugaban NSC, Shehu Dikko, ke jagoranta tare da karuwar tallafin Gwamnatin Tarayya domin ciyar da harkokin wasanni matakin gaba.
Sai dai Najeriya ta kammala da zinare 10 kawai wanda ya yi kasa da abin da aka yi hasashen kuma ya ragu da zinare 2 idan aka kwatanta da zinare 12 da aka samu a Birmingham a 2022. Jimillar lambobin yabo ma ya ragu daga 35 a Birmingham zuwa 24 a Glasgow.
Duk da rashin cimma wadannan burin, Tawagar Najeriya ta yi gagarumar nasara kuma ta fadada inda take samun lambobin yabo zuwa wasanni irin su: wasan guje-guje da tsalle-tsalle da wasan judo da daukar karfe mai nauyi da wasannin masu bukata ta musamman na guje-guje da tsalle-tsalle da daukar karfe mai nauyi da sauran su.
Domin kara wa ’yan wasa kwarin gwiwa yayin gasar, Hukumar Wasanni ta Kasa ta fitar da sabon tsarin bayar da kyaututtuka nan take a tsakiyar gasar.
Shugaban NSC, Shehu Dikko, ya amince da kara kyautar lambobin yabo, inda ya kara kyautar wadanda suka lashe zinare zuwa dala 10,000. Dala 5,000 tsabar kudi nan take da kuma dala 5,000 da za a biya a asusun ’yan wasan.
Wadanda suka samu azurfa sun samu dala 5,000, yayin da masu tagulla suka samu dala 3,000. Masu horar da wadanda suka lashe zinare ma sun samu dala 5,000, bayan alawus na yau da kullum na dala 200 ga ’yan wasa da dala 250 ga masu horarwa.