Wasu masana kimiyyar siyasar Najeriya sun ce babu abin da PDP za ta taɓuka a Zaɓen Shugaban Ƙasa na 2027.
Dokta Abubakar Umar Kari, ɗaya daga cikin masanan da suke da wannan fahimta, ya kafa hujja da ingancin mutumin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta amince ya yi wa jam’iyyar takara yana nuni da cewa kowa ya sayi rariya ya san za ta zubar da da ruwa.
“Ɓangaren [Ministan Abuja Nyesom] Wike na jam’iyyar PDP dai ungulu ne da kan zabo….
“Da ma abin da ake zargi… shi ne cewa ko dai su haɗa kansu da [APC ya zama ba su da ɗan takara], ko kuma su samu wani mai rauni wanda ba inda zai je a ba shi wannan aikin,” inji Dokta Kari.
-
Yunkurin Tinubu na inganta masana’antu na samun nasara – Ministan Yada Labarai
-
Najeriya a shirye take don huldar zuba jari da cinikayyar zamani da Saudiyya
Wannan fashin baƙi yana zuwa ne bayan da INEC ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da jam’iyyun siyasa suka tsayar domin fafatawa a babban zaɓen baɗi.
Jerin sunayen dai ya nuna cewa INEC ta sanya sunan ɗan takarar shugaban ƙasa na ɓangaren Wike, [PLEASE MENTION HIS NAME HERE], maimakon na ɓangaren Kabiru Tanimu Turaki, duk da cewa rikicin shugabancin jam’iyyar da ya shafi batun yana gaban kotu.
Sai dai masanin ya ƙara da cewa a ganinsa jam’iyyar ta PDP za iya taka muhimmiyar rawa a wasu ba a zaɓen zaɓuɓɓukan har ma ta samu wasu kujerun ‘yan majalisar dokoki da kuma wasu muƙaman siyasa.
A wata hira da ya yi da Blueprint Radio a Abuja, Dokta Kari ya ce INEC ce kaɗai ta san dalilin da ya sa ta fitar da sunan ɗan takarar ɓangaren Wike maimakon na ɓangaren Kabiru Tanimu Turaki.
“Lauyoyi da dama da kuma masu ilimin shari’a sun bayyana cewa babu wani hukuncin kotu da ya wajabta hakan.
“A taƙaice, daga kotunan da suka saurari shari’ar har zuwa Kotun Ƙoli, babu inda aka yanke hukunci a fili da ya ce a bai wa ɓangaren Wike takarar shugaban ƙasa,” a cewar masanin.