Ministan Labarai da Wayar da Kan Al’umma na Kasa, Mohammed Idris, ya bayyana cewa kofar Najeriya a bude take don kasuwanci da  zurfafa hadin gwiwa a fannonin zuba jari da cinikayyauj da yawon bude ido da Masarautar Saudi Arabiyya, yayin da Tsarin Sabon Fata (Renewed Hope Agenda) na Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ci gaba da samar da sabbin damammaki na bunkasar tattalin arziki da hadin gwiwar kasa da kasa.

Da yake jawabi a ranar Talata a taron Baje Kolin Zuba Jari da Yawon Bude Ido na Kasashen Waje tsakanin Najeriya da Saudi Arabiyya (Nigeria–Saudi Diaspora Investment and Tourism Exhibition Summit 2026) da aka gudanar a Abuja, Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya tana aiwatar da garambawul mai karfi da nufin gina tattalin arziki mai gasa da abokantaka ga masu zuba jari, wanda sana’o’i da kirkire-kirkire da bunkasar kamfanoni masu zaman kansu ke tafi da shi.

“Najeriya a bude take don kasuwanci kuma a shirye take don zurfafa hadin gwiwa da Saudi Arabiyya. Garambawul dinmu na tattalin arziki yana samar da sabbin damammaki na zuba jari, cinikayya, da yawon bude ido, kuma muna gayyatar masu zuba jari da su amfana da dimbin damar da kasarmu ke bayarwa,” in ji Ministan

Muhammaf Idris ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin dandamali ga gwamnatoci da  masu zuba jari, da kamfanoni masu zaman kansu don kulla kawance na azo-a-gani wanda zai fadada kasuwanci, ya zaburar da zuba jari, ya samar da ayyukan yi, sannan ya karfafa alakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Ya ce Tsarin Sabon Fata na Shugaba Tinubu yana sauya fasalin fannin zuba jari na Najeriya ta hanyar garambawul na dabara a fannonin ababen more rayuwa da fannoni daban-daban na tattalin arziki da aikin gona da tallafin kudin ilimi da kirkire-kirkiren fasahar zamani da  bunkasa kwarewa, da kuma inganta tsaro.

A cewar Ministan, wannn  garambawul din na aza harsashin dorewar bunkasar tattalin arziki tare da daukaka darajar Najeriya a matsayin guri mafifici kuma abin zaba don zuba jari na shiyya-shiyya da na duniya.

“Nauyinmu ne mu ci gaba da nuna sahihiyar sura, madaidaciya, kuma mai cike da kwarin gwiwa game da Najeriya. Zuba jari yana bunkasa ne inda aka samu gaskiya da  daidaiton manufofi, da amana. Mun himmatu wajen tabbatar da cewa duniya ta ga ainihin abin da Najeriya take—kasa ce mai dimbin damammaki, juriya, da alkawari na gari,” in ji shi.

Ministan ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ke takawa a matsayin jakadun karfin tattalin arzikin kasar, inda ya lura cewa kwarewarsu, hanyoyin sadarwar kwararru, da nasarorin kasuwanci suna ci gaba da karfafa huldar kasashen biyu da jawo zuba jari zuwa Najeriya.

Ya bukaci mahalarta taron da su fassara tattaunawar zuwa sakamako na gaske ta hanyar kara zuba jari, musayar fasaha, bunkasa yawon bude ido, kawancen kirkire-kirkire, da hadin gwiwar kasuwanci (joint ventures) wadanda za su kawo fa’ida mai dorewa ga kasas8hen biyu.

“Bari mu matsa gaba daga tattaunawa zuwa aikatawa. Bari mu gina kawance da zai samar da ayyukan yi, ya bunkasa kasuwanci, ya daukaka kirkire-kirkire, sannan ya inganta rayuwar mutanenmu,” in ji Ministan.

A nata jawabin, Shugaba/Babban Jami’ar Hukumar ‘Yan Najeriya mazauna Kasashen Waje (NiDCOM), Hon. Dr. Abike Dabiri-Erewa, ta yi kira da a karfafa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Najeriya da Saudi Arabiyya ta hanyar zuba jari da ‘yan kasashen waje ke jagoranta. Ta bukaci masu zuba jari da su bincoki damammaki a fannonin gidaje (real estate) da aikin gona da yawon bude ido da sufuri da adana kaya (logistics), da sauran muhimman fanni, tana mai jaddada cewa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje sun kasance abokan tarayya masu muhimmanci a ci gaban kasa.

“Gudunmawar da ‘yan kasashen waje ke bayarwa ta wuce tura kudi gida kawai. Suna kawo kwarewa ta duniya, bayanan kasuwa, amana, da manyan hanyoyin sadarwa wadanda za su iya bude kofofin zuba jari da samar da ayyukan yi. Bari mu wuce batun tattaunawa zuwa ga hadin gwiwa na aiki wanda zai karfafa alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Saudi Arabiyya,” in ji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *