Bruno Guimaraes.

Arsenal ta kusa kammala yarjejeniyar da ta daɗe tana ƙoƙarin yi don sayan kyaftin ɗin Newcastle United, Bruno Guimaraes.

A halin yanzu, Guimaraes na jiran izini ne kawai don barin sansanin horas da ‘yan wasan Newcastle da ke La Manga, da ke ƙasar Spaniya, domin kammala sauran matakai na komawar sa zuwa Filin wasa na Emirates.

A na sa ran Gunners za ta yi wa dan wasan tsakiyar Brazil gwajin lafiya a wannan mako. Sai dai ba a tabbatar da kuɗin sayarwa ba tukuna, amma majiyoyi na nuni da cewa zai iya kai fam miliyan 80.

Guimaraes, wanda ya koma Newcastle daga Lyon a 2022, ya bayyana niyyar sa ta komawa Arsenal da taka leda.

Ɗan wasan mai shekara 28 yanzu shi ne ɗan wasan tsakiya da kocin Arsenal, Mikel Arteta ke burin saya.

Tuni dai Newcastle da Arsenal suka tattauna kan sauran sharuɗan yarjejeniyar sayar da ɗan wasan a wannan mako, kuma ana sa ran za a kamala komai cikin sauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *