Salah tare da magoya bayan kungiyar Trabzonspor ta Turkiyya

Ƙungiyar Trabzonspor ta Turkiyya, na shirin tabbatar da sanya hannu kan sayan Mohamed Salah, yayin da kyaftin ɗin na ƙasar Masar ya gamu da tarba mai ban mamaki daga magoya baya lokacin da ya sauka a Turkiyya.

Ɗaruruwan magoya baya ne suka taru a wajen Filin Jirgin Sama na Ataturk da ke Istanbul a ranar Laraba, yayin da Salah ya fito sanye da kayan Trabzonspor sannan ya gana da su cikin murna da fara’a.

Salah, ɗan wasan gaba mai shekara 34 ya bar Liverpool a ƙarshen kakar da ta gabata bayan ya kwashe shekaru 9 a Merseyside, inda ya zura ƙwallaye 257.

Ba a san nawa Salah zai samu a Trabzonspor ba tukuna, amma dai ana sa ran kungiyar za ta iya mayar da shi ɗan wasan da ya fi kowa ɗaukar albashi mai tsoka.

Salah, wanda ya zura ƙwallaye 50 a Gasar Zakarun Turai, zai buga Gasar yankin Turai tare da Trabzonspor a kakar wasa mai zuwa bayan sun ƙare a matsayi na 3, da maki 8 a bayan zakarar gasar, Galatasaray.

Idan kuma suka kasa wuce wa zuwa matakin rukuni na Gasar Europa League ta hanyar wasannin neman tikiti, za su koma buga Gasar Conference League.

Trabzonspor ta lashe gasar ƙasar Turkiyya sau 7, 6 daga cikinsu sun zo tsakanin 1976 da 1984.

A 2022 suka sake lashe gasar, inda suka kawo ƙarshen jiran shekaru 38 da suka yi rabuwar su da lashe gasar.

A lokacin da yake Liverpool ya taimaka musu lashe Kofin Firimiyar Ingila sau 2, da Gasar Zakarun Turai 1, da Club World Cup, da UEFA Super Cup, da FA Cup da kuma EFL Cup sau 2.

Har ila yau a ƙasar Ingila, Salah ya lashe Takalmin Zinare na Gasar Firimiya sau 4, sannan an zaɓe shi a matsayin ɗan wasan shekara na PFA sau 3 – a 2018, da 2022 da kuma 2025.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *