Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta umarci bankin First Bank da ya dakatar da duk wata mu’amala a asusun gwamnatin jihar Osun.

Gwamnan jihar, Sanata Ademola Adeleke, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Osogbo, inda ya soki matakin yana mai cewa an bada umurnin tare da umarnin kotu ba.

A cewar Gwamnan, wasiƙar EFCC mai ɗauke da kwanan watan 5 ga Agustan 2026, wadda Daraktan Bincike na hukumar, Adenike S. Babalola, ta sanya wa hannu, ta umarci bankin da ya sanya takunkumin cire kudi a asusun gwamnatin jihar, bisa tanade-tanaden Dokar Kafa hukumar EFCC ta 2004 da kuma Dokar Yaki da cire Kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba ta 2022.

Adeleke ya danganta matakin da yunkurin yin tasiri kan zaɓen Gwamnan jihar da ake shirin gudanarwa ranar 15 ga Agusta, yana mai cewa hakan barazana ce ga dimokuraɗiyya da bin doka a jihar Osun.

Ya kuma ce ya umarci Babban Lauyan Jihar, Barista Jimi Bada (SAN), da ya kalubalanci matakin a Babbar Kotun Tarayya da ke Osogbo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *