Dan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Accord, Farfesa Christopher Imumolen, ya janye daga takarar domin mara wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC baya.

A cikin wata sanarwa da Farfesa Christopher Imumolen ya fitar a ranar 2 ga Agusta, 2026, ya ce bayan zaɓen da aka yi masa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Accord a zaɓen fidda gwani, sun tattauna da shugabannin jam’iyyar sa inda suka yanke shawarar marawa Tinubu baya, domin fifita kishin kasa.

Imumolen ya ce suna da manufofi iri guda da Shugaban, musamman a bangaren bunƙasar tattalin arziki, ilimi, matasa, harkokin kasuwanci, masana’antu da raya ƙasa.

Ya ce Shugaba Tinubu na da ƙwarewar jagoranci na musamman, juriyar yadda yake tafiyar da matsalolin Najeriya na nuna ƙarfin hali, jajircewa da dabarun shugabanci da ya kamata a yi koyi da su.

“Tinubu na da ƙwarewar siyasa ta musamman, domin a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya, shugaban  ya na da hikima, hangen nesa da kuma fasahar gina ƙasa, waɗanda sun taimaka wajen samar da shugabanni masu tasiri a sassa daban-daban na ƙasar” Inji shi

Manufofin shugaban ƙasar na inganta tsarin mulki, kyautatawa da dunkule hukumomi masu kamanceceniyar aiki da juna, su ke baiwa manazarta kwarin gwiwar ganin Najeriyar da ake fata anan gaba a cewar sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *