Harabar Kotun kolin Najeriya dake Abuja

Kotun Kolin Najeriya ta jinkirta yanke hukunci a kan wasu kararraki guda biyu dake gabanta, wadanda bangaren Kabiru Tanimu Turaki na jam’iyyar PDP da Gwamna Seyi Makinde ke marawa baya ya shigar.

Masu daukaka karar sun nemi a soke wani hukunci na Kotun Daukaka Kara, wanda ya rushe Babban Taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a birnin  Badun na Jihar Oyo a watan Nuwamban shekarar da ta gabata.

Alkalai biyar na Kotun a karkashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba ne suka sanar da hakan ranar Laraba, inda suka bayyana cewa za a sanar da lauyoyin bangarorin biyu ranar da za a yanke hukunci nan gaba.

Tun da fari, jam’iyyar PDP ce ta shigar da kara tana kalubalantar matsayin Kotun Daukaka Kara, wadda ta tabbatar da hukuncin Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, wanda ya haramta wa jam’iyyar gudanar da Babban Taronta na Kasa ba tare da sanya tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido a cikin ‘yan takara ba.

A daya bangaren kuma, ita ma uwar jam’iyyar ta kasa ta shigar da kara tana kalubalantar hukuncin Mai Shari’a James Omotosho, wanda ya haramta wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) sanya ido a kan taron na Badun har sai an cika wasu sharuddan shari’a.

A yanzu haka, dukkan lauyoyin bangarorin biyu sun gabatar da hujjojinsu a gaban kotu, inda kowane bangare yake fatan samun nasara.

Daga nan ne Kotun ta jingine shari’ar tare da fadin cewa za ta sanar da wani lokaci anan gaba domin yanke hukuncin karshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *