Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da ɗaurin auren zawarawa 1,500 a ranar Juma’a, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsaya wa Mutumin da aka kashe wa iyalan sa a Unguwar Dorayi Malam Haruna Bashir a matsayin waliyyi.
Malam Haruna Bashir, ya rasa iyalan sa ne bayan wani harin ta’addanci da wasu matasa suka kai kan iyalan sa a farkon shekarar 2026, kuma tuni aka gabatar dasu gaban Shari’a.
Daurawa Malam Haruna aure na daga cikin alkawurran da gwamnatin jihar Kano ta dauka, bayan kai shi Umara da kuma aikin Hajji, tare da ba shi gida a Amana City da ke birnin Kano.
A yau kuma gwamnatin jihar ta cika masa alkawari na karshe inda aka sake daura masa aure da Nabila Kabiru Yunusa a gagarumin bikin da aka gudanar a Masallacin Juma’a na Fadar Mai Martaba Sarkin Kano.
Har ila yau an gudanar da makamancin ɗaurin auren lokaci guda a ƙananan hukumomin jihar 44, ƙarƙashin shirin auren zawarawa da gwamnatin jihar ke biya sadakin Naira dubu dari 2, kayan daki da kuma jari ga Amaren.
- Ƙungiyar tsofaffin sojoji za ta taimaka wajen daƙile yaduwar ƙananan makamai
- Hotuna: Asarar da Gobara ta jawo a Gidan Mai na AY Shafa dake Garki Abuja
- Kawar da haramtattun tashoshin ɗaukar fasinja a Birnin Tarayyar Najeriya
Da yake jawabi a wajen taron, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa gwamnati ta kuma ba Haruna Bashir ƙarin tallafi domin taimaka masa ya sake gina rayuwarsa bayan wannan mummunan rashi.
Ya ce an ɗauki waɗannan matakai ne domin rage masa raɗaɗin da ya samu sakamakon rashin iyalansa, tare da ba shi damar fara sabuwar rayuwa.
Daurawa ya kuma yi kira ga sabbin ma’auratan da su kiyaye mutuncin aure, su zauna lafiya da juna, tare da gina iyalai nagari da za su kasance masu amfani ga al’umma.
Gwamnatin Jihar Kano ta ware kimanin naira miliyan 300 domin wannan sabon zagaye na shirin ɗaurin auren gama-gari, wanda aka ƙaddamar domin tallafa wa zawarawa da sauran waɗanda suka cancanta a faɗin jihar.