Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya jaddada goyon bayan sa ga takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Zaɓen gama-gari na 2027.
Adeleke ya bayyana hakan ne a Osogbo, yayin da yake yi wa manema labarai jawabi, bayan ayyana shi da INEC ta yi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a jihar ta Osun.
Ya godewa Shugaba Tinubu a saboda tsaiwar dakan da ya yi wajen ganin an tabbatar da sahihin zaɓe a jihar, yana mai tunatar da jama’a cewa, kar su manta fa Shugaba Tinubu ɗan asalin jihar Osun ne.
- Da Dumi-Dumi: Adeleke ya lashe zaɓen gwamna na Osun
- WAFCON 2026: Aljeriya ta lashe tagulla bayan ta casa Marokko
- Zaɓen Osun 2025: An fara tattara sakamako a rumfunan zaɓe
Adeleke ya kuma godewa ɗaukacin al’umar jihar ta sa a saboda jajircewar su wajen ganin an tabbatar tare da kare tsarin dimukuraɗiyya.
Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Osun ɗin ya kuma yi alƙawarin ba zai juya wa al’umar jihar baya ba, a yanzu da suka sake ba shi damar ƙara mulkar su a karo na biyu.
Da sanyin safiyar Lahadin nan ne dai INEC ta ayyana Ademola Adeleke, gwamnan jihar Osun mai ci, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar, 15 ga Agustan 2026.
Da yawa na yi wa zaɓen kallon wani fage da aka fafata tsakanin jam’iyya mai mulki a jihar, Accord da kuma APC, inda su kai ta tafiya dab da juna, har a ƙarshe, jam’iyyar ta Accord ta samu rinjayen kuri’un da ya ba ta damar lashe zaɓen.
An kuma bayyana zaɓen da cewa ya gudana cikin lumana, kuma sakamakon sa ya gamsar.