Ɗan takarar Jam’iyyar Accord a zaɓen gwamnan Jihar Osun na 2026 kuma gwamna mai ci, Ademola Adeleke, ya lashe zaɓen gwamnan jihar wanda aka gudanar ranar Asabar, 15 ga watan Augustan 2026.

Babban mai sanar da sakamakon zaɓe na gwamnan Jihar Osun na 2026, Farfesa Joshua Olalekan Ogunwole, shi ne ya sanar da hakan da safiyar ranar Lahadi, daga cibiyar tattara sakamakon zaɓe dake Osogbo.

A cewar Farfesa Ogunwole, gwamna Adeleke ya samu ƙuri’u 511,067, inda ya doke ɗan takarar jami’yyar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu ƙuri’u 444, 815.

Wannan na nuni da cewa Gwamna Adeleke na Jam’iyyar Accord ya doke babban abokin hamayyar sa na Jam’iyyar APC, Oyebamiji, da ta tazarar ƙuri’u 66,252.

Har wayau, Farfesa Ogunwole, ya sanar cewa ɗan takarar jami’yyar ADC, Najeem Salam, ya samu ƙuri’u 17, 180.

Da wannan ne, Farfesa Ogunwole, ya bayyana gwamna mai ci a yan zu, Adeleke, a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya samu ƙuri’u masu rinjaye a kan abokan hammayyarsa a zaɓen.

Ana yi wa Ademola Adeleke laƙabi da “Dancing Senator” wato, Sanata Mai Rawa saboda yadda yakan saki jiki ya taka rawa yayin yaƙin neman zaɓe.

Adeleke, na Jam’iyyar Accord, ya fara tsaya wa zaben gwamnan Jihar Osun a shekara ta 2018, a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP amma ya yi rashin nasara a hannun Gboyega Oyetola na APC.

Adeleke ya sake dawo wa takarar gwamna a 2022, inda ya sake fuskantar Oyetola, wanda shi ne gwamna mai ci a wancan lokacin, amma a wannan karo ya doke Oyetola.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *