Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya (FCTA) tace ta ɗauki matakai domin magance matsalar ambaliyar ruwa da ke addabar wasu sassan Abuja.
Babban Mataimaki na Musamman ga Ministan Abuja kan Hulɗa da Jama’a da Kafofin Sadarwa, Lere Olayinka, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.
Olayinka na mayar da martani ne kan kalaman wani lauya, Deji Adeyanju, wanda ya zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da lalata Abuja.
- Cardoso, Ojulari, Tantita za su karɓi lambobin yabo na Blueprint Newspapers
- Wani Fasto ya karrama wani malamin Addinin Musulunci a Najeriya
- Adeleke: Har yanzu Oyebamiji bai taya ni murna ba
Kalaman Adeyanju sun biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi ranar Asabar, wanda Olayinka ya ce ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassan Abuja.
Sai dai ya ƙara da cewa ruwan ya janye bayan ruwan saman ya tsaya.
Ya ce gwamnatin FCT da Wike ke jagoranta tana sane da wannan matsala kuma ta ɗauki matakan da suka dace domin hana sake faruwar irin hakan nan gaba.