Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya taya tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, murnar cika shekaru 85 da haihuwa, inda ya bayyana shi a matsayin dattijon ƙasa da rayuwarsa ta kasance muhimmin sashe na tarihin Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ministan ya ce tarihin Babangida na aikin soja da jagorancin ƙasa da kuma rayuwarsa a matsayin ɗan ƙasa mai kishin kasa, ya taka muhimmiyar rawa wajen sauye-sauyen siyasa da hukumomi a Najeriya.
Mohammed Idris ya ce duk da cewa Babangida ya bar mulki shekaru da dama da suka gabata, har yanzu yana ci gaba da bayar da gudunmawa kan batutuwan da suka shafi haɗin kan Najeriya da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
- Toshewar hanyoyin ruwa na ƙara ta’azzara matsalar ambaliya a Abuja
- NDLEA ta kama motar safa cike da muggan ƙwayoyin sama da 370,000
Ya bayyana kwarewar tsohon shugaban a fannin jagoranci da hidimar jama’a a matsayin wata taska da matasa da shugabanni na baya da masu zuwa za su iya koya daga gare ta wajen fahimtar ƙalubalen gina ƙasa.
Ministan ya kuma yaba da yadda Babangida ke nuna imani da Najeriya tare da ci gaba da yin kira da samar da haɗin kai da zaman lafiya tsakanin ’yan ƙasa.
Mohammed Idris ya ce, “Janar Babangida na ci gaba da kasancewa muhimmiyar murya a tafiyar ƙasarmu, kuma yayin da ya cika shekaru 85, muna murnar hidimarsa da dattijantakarsa da kuma jajircewarsa wajen ganin Najeriya ta kasance ƙasa ɗaya.”
Ministan ya yi wa tsohon shugaban fatan ƙarin shekaru masu yawa cikin koshin lafiya, zaman lafiya da walwala, tare da fatan ya ci gaba da samun ƙaunar iyalansa da mutunta ’yan Najeriya.