Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, Alhaji Ibrahim Musa Gusau, ya ƙaddamar da sabon kwamitin da zai gudanar da sahihin bincike akan matsalolin da suke hana harkar ƙwallon ƙafa na Najeriya ci gaba.

Alhaji Ibrahim Musa Gusau ya buƙaci mambobin kwamitin da su yi aiki cikin gaskiya da kuma jajircewa domin ci gaban ƙasar.

Bayan gazawar tawagar ‘yan matan Najeriya, wato Super Falcons, na samun tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya na Mata na shekara mai zuwa, NFF ta kafa wannan kwamitin a ranar Juma’a da ta gabata domin gano tushen matsalar da ya hana Najeriya taɓuka abun azo a gani a wasannin ƙasa da ƙasa a baya-bayan nan, da kuma musamman cire Super Falcons a Gasar WAFCON.

A cewar Gusau, “ku binciki ko me nene dalilan da yasa tawagun mu na ƙasa ƙoƙarin su ya gaza a wasannin ƙasa da ƙasa na baya-bayan nan, kuma musamman gazawar da ba a zata ba ta Super Falcons na rashin samun tikitin zuwa Gasar Duniya. Ku na da makonni biyu domin kammala aikin da kuma miƙa rahoto.”

“Mun kafa wannan kwamitin ne saboda mun yi imanin cewa za ku kawo hanyoyin magance wannan matsala, la’akari da rawar da kowa daga cikinku ya taka a wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya tsawon lokaci.”

Shugaban kwamitin, Ambasada Fanny Ikhayere Amun, ya yi alƙawarin za su gudanar da aikin su cikin gaskiya, sannan za su tattauna da mutanen da abin ya shafa, kuma za su karɓi shawarwari daga al’umma.

“Muna kallon wannan a matsayin muhimmin gayyata don yiwa ƙasa aiki. Ba abin da za a yi rabi-da-rabi ba ne. Dole mu shiga cikin aikin da karfinmu, mu fitar da rahoto da duk masu ruwa da tsaki a wasannin Najeriya za su yi alfahari da shi. Dole mu faɗi gaskiya a kowane lokaci, mu kuma yi aiki cikin jajircewa,” in ji Ikhayere.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da
tsohuwar kyaftin din Super Falcons, wadda ta lashe kofin mata na Afirka sau 4 kuma ta buga Gasar Duniya, Desire Oparanozie; da
tsohon kyaftin din Super Eagles, wanda ya lashe zinari, azurfa da tagulla na AFCON kuma ya buga Gasar Duniya, Mutiu Adepoju; da
tsohon kocin tawagar ‘yan kasa da shekaru 20 na Najeriya kuma shugaban kungiyar masu horar da kwallon kafa ta Najeriya, Ladan Bosso.

Sauran sun haɗa da tsohon alƙalin Hukumar FIFA kuma tsohon shugaban sashen nazarin gudanarwa a Cibiyar Wasanni ta Ƙasa, Dr Alex Mana.
Sakataren kwamitin shine tsohon ɗan wasan Najeriya kuma mataimakin darekta a sashen horaswa na NFF, Nasiru Jibril.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *