Sanata Kabiru Marafa ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar (ADC), inda ya koma sabuwar jam’iyya mai suna (NDC), makonni kadan bayan barinsa jam’iyyar (APC) mai mulki sakamakon rashin jituwa da aka samu a cikin gida.
Sanata Marafa, wanda ke da burin tsayawa takarar Gwamnan Jihar Zamfara, ya dauki wannan mataki ne bayan rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar ADC ta ki bashi tikitin takarar gwamna.
Bayanan da muke samu sun nuna cewa tsohon Sanatan ya koma jam’iyyar NDC ne bayan an tabbatar masa da cewa zai samu tikitin tsayawa takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar domin fafatawa a zaben dake tafe.
Duk da cewa jam’iyyar ADC bata ce komai akan wannan mataki da Sanata Kabiru Marafa ya dauka ba, ganin cewa bai dade da komawa cikin jam iyyar ba, har ila yau babu wata sanarwa a hukumance dake nuna jam iyyar na da wani dan takara a jihar Zamfara.
A baya bayan nan ana rade radin cewar wasu jiga jigan yan siyasa na duba yiwuwar tsallakawa zuwa sabuwar jam iyyar NDC, sakamakon alamun rashin makoma a sauran jam iyyun hamayya da yanzu haka ke zaman jiran matsayin su a gaban kotuna daban daban
