Rundunar ’yan sandan Jihar Sokoto ta ce ta kashe ’yan bindiga biyu tare da cafke wasu mutane tara da ake zargi da hannu a aikata laifuka daban-daban, ciki har da satar babura, garkuwa da mutane da kuma sauran laifukan ta’addanci.

Rundunar ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kakakin ’yan sandan Jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, ya gudanar a ranar 19 ga Agusta, 2026, a madadin Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Hayatu Hassan Shaffa.

A cewar rundunar, a ranar 15 ga Agusta da misalin ƙarfe 9 na dare, an samu rahoton cewa wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai na kokarin kai hari kauyen Dankadu da ke karamar hukumar Illela, bayan sun taso daga dajin Tsauana.

Rundunar ta ce jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane da sauran jami’an tsaro sun hanzarta zuwa wurin, inda suka yi arangama da ’yan bindigar. Bayan musayar wuta mai tsanani, ’yan bindigar sun tsere zuwa cikin daji dauke da raunukan harbin bindiga.

Bayan jami’an tsaron sun binciki dajin, sun ce sun samu nasarar kashe biyu daga cikin ’yan bindigar tare da kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da harsasai 54

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *