A halin yan,i, rundunar ’yan sandan Jihar Sokoto ta ce, ta cafke mutane uku da ake zargi da kasancewa cikin wata kungiyar da ta kware wajen satar babura a wasu sassan birnin Sokoto.

Waɗanda aka cafken sun hada da Siba Abdullahi daga Dimbiso a karamar hukumar Wurno da Hassan Hassan daga yankin Tamaje da Usama Isah daga Unguwar Rogo a Sokoto.

Binciken gidajensu ya kai ga gano babura biyar da ake zargin an sace, da kuma bindigar hannu guda da aka kera ba bisa ka’ida ba.

Rundunar ta ce an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Haka kuma, rundunar ta ce ta kama wasu mutane biyu, Hamza Abubakar da Yasir Muhammed, bayan samun rahotannin karuwar satar babura, karbar haraji ba bisa ka’ida ba da kuma safarar miyagun kwayoyi a wasu yankunan Mana Babba, Mabera, Unguwar Rogo da Tamaje

Binciken da aka gudanar ya kai ga gano wasu mutane da ake zargi da hada baki wajen satar babura da sayar da su, inda rundunar ta ce har yanzu ana farautar wasu daga cikin wadanda ake zargin.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *