Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Asabar ta fitar da jerin sunayen mambobin Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa Na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

An tsara gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a watan Janairun 2027, kamar yadda jadawalin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar ya nuna.

Wata sanarwa da Bayo Onanuga, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai kasance Shugaban Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, wanda ake sa ran zai kasance abokin takarar Tinubu a zaɓen 2027, zai kasance Mataimakin Shugaban Majalisar.

An kuma naɗa Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari, shi ne ya zamo Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen.

Gwamnan Jihar Imo kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Progressive Governors’ Forum, Hope Uzodinma, ya zama Sakataren Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen.

Sakataren APC na Ƙasa, Ajibola Bashiru, da Hadiza Bala-Usman za su kasance Mataimakan Sakataren.

Yayin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, aka ɗora musu alhakin kasancewa Mataimakan Daraktocin-Janar na yaƙin neman zaɓen a Kudu da Arewa.

Za su yi aiki tare da Sanata Bamidele Opeyemi da Sanata Jibril Barau a shiyyoyin biyu.”

Sanata Adams Oshiomhole zai kasance Mataimakin Darakta-Janar mai kula da tattara magoya baya, yayin da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa zai kasance Mataimakin Darakta-Janar mai kula da harkokin gudanarwa.”

James Abiodun Faleke, wanda ya taka muhimmiyar rawa a yaƙin neman zaɓen 2022/2023, ya dawo a matsayin Mataimakin Darakta-Janar mai kula da tsare-tsaren zaɓe, daidaitawa da sa ido.

Faleke zai yi aiki tare da daraktocin shiyyoyi, inda Sanata Olushola Adeyeye zai kula da Kudu maso Yamma, Dr. Ngozi Olejeme da Kudu maso Kudu, Sanata Uche Ekwunife da Kudu maso Gabas, Muntaqha Rabe da Arewa maso Yamma, Ahmed Muhammed Getso da Arewa ta Tsakiya, yayin da Sanata Sani Danladi zai kula da Arewa maso Gabas.

Ita kuwa Stella Okotete, da Injiniya Abdullahi Garba Ramat da Audu Maikori za su kasance Sakataren Daraktar Tsare-tsaren Zaɓe.

Muiz Adeyemi Banire zai jagoranci Sashen Shari’a a matsayin Darakta, tare da Dr. Liman Hassan da Babatunde Ogala a matsayin mataimakansa. Sauran mambobin sashen sun haɗa da Prince Lateef Fagbemi, tsohon Gwamnan Jihar Katsina Ibrahim Shema, Worgu Boms da Dr. Kingsley Tochukwu Udeh.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris Malagi, zai kasance Darakta mai Kula da Haɗa Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwar, tare da Dele Alake, Bayo Onanuga da Lanre Issa-Onilu.

Sashen Yaɗa Labarai ya kuma ƙunshi Tunde Rahman, Sunday Dare, Daniel Bwala da Felix Morka, waɗanda aka naɗa a matsayin Mataimakan Daraktoci Masu Daidaita Ayyuka.

Sanarwar ta ƙare da cewa “Yayin da muke shiga lokacin yaƙin neman zaɓe, muna da nasarori da dama da za mu bayyana. Mu nuna tarihin ayyukanmu cikin ƙarfin gwiwa, mu kuma ƙarfafa fata a kowane lungu na ƙasarmu. Mu kayar da dukkan waɗanda ke shirin mayar da ƙasarmu baya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *