Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya amince da naɗin da aka yi masa a matsayin Darakta Janar na Kwamitin Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) don zaɓukan shekarar 2027.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja, sanatan na Zamfara ta Yamma ya bayyana matuƙar godiyarsa da kuma yadda yake ɗaukar wannan nauyi da muhimmanci.

“Na karɓi wannan nauyi da matuƙar godiya da kuma cikakken muhimmanci. Godiya ta musamman tana zuwa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma jam’iyyar saboda amana da aka ba ni, haka kuma ga shugabannin jam’iyyarmu saboda kwarin gwiwa da suka nuna mini.

“Ba na ɗaukar wannan abun da wasa,” in ji Yari.

Ya bayyana kamfen a matsayin wani abu da ya wuce zaɓe kawai, inda ya kira shi da “tattaunawa da al’ummar Najeriya a kowace jiha, kowane yare, da kowane addini game da makomar da muke gina wa tare.”

Yari ya yi alƙawarin cewa za a gudanar da kamfen ɗin cikin ladabi, haɗin kai, da kuma girmama kowa da kowa.

Ya bayyana cewa aiki ya fara nan da nan kuma akwai gurbi ga kowa da kowa.

Ga ‘yan Najeriya na kowane ɓangaren siyasa, ya yi kira gare su da su zaɓi ci gaba maimakon rarraba kai, ya kuma ƙara da cewa jam’iyyar za ta sami amincewar jama’a ta hanyar ayyukanta na gani da ido maimakon surutu

.“Da yardar Allah, kuma da ƙoƙarinmu baki ɗaya, za mu samu nasara a watan Janairun 2027,” ya kammala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *