Ƙasar Syria na sa ran za a sake fara tattaunawa nan ba da jimawa ba da Isra’ila kan wata yarjejeniyar tsaro da take fatan za ta kai ga janye sojojin Isra’ila daga ƙasar Syria.

Wani babban jami’in gwamnatin Syria ya kuma bukaci Isra’ila ta yi amfani da abin da ya kira “damar tarihi”, kasancewar har yanzu ƙofar diflomasiyya a buɗe take.

A wata hira da kamfanin dillancin labaran Reuters a Damascus ranar Asabar, kwanaki kaɗan bayan Isra’ila ta kai hari ta sama kan wani sansanin sojin saman Syria, Ministan Harkokin Wajen Syria Asaad Al-Shaibani ya ce babban abin da Damascus ta fi mayar da hankali a kai shi ne dakatar da hare-haren Isra’ila.

Ya ce ana buƙatar ɗaukar matakan gina amincewa tsakanin ɓangarorin biyu domin cimma wannan buri.

Amurka ta shafe sama da shekara tana ƙoƙarin samar da wata yarjejeniyar tsaro tsakanin Isra’ila da gwamnatin Shugaban Syria Ahmed Al-Sharaa, wanda yanzu Amurka ke ɗauka a matsayin sabuwar ƙawarta a Gabas ta Tsakiya.

Sai dai har yanzu ba a samu cimma yarjejeniyar ba, yayin da Isra’ila ta tura sojojinta cikin yankunan Syria tare da kai hare-hare kan kadarorin gwamnatin Syria, tana mai cewa hakan ya zama dole domin kare tsaron ƙasarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *