Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa da sauran al’amura, Ibrahim Masari, ya ce kusan malaman Musulunci da shugabannin addini 500 sun amince da Shugaba Tinubu ya sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Masari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaransa ya fitar, wadda ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar, bayan halartar taron malaman addini a Dutse, Jihar Jigawa.

A cewar sanarwar, taron wanda aka gudanar a ɗakin taro na  Sir Ahmadu Bello dake Dutse, ya haɗa malaman Musulunci, masana, shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki daga jihohin Arewa 19 da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Rahotanni sun ce mahalarta taron sun tattauna kan matsalolin tsaro, tattalin arziki da zamantakewa, da kuma ci gaban yankin Arewa.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai gwamnonin Jigawa, Umar Namadi; Kano, Abba Yusuf; Yobe, Mai Buni; Sokoto, Ahmad Aliyu; da Kaduna, Uba Sani.

Haka kuma, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, da Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Muttaka Darma, sun halarci taron.

Mahalartan taron sun kuma jaddada muhimmancin haɗin kan ƙasa, zaman lafiyar siyasa da kuma kyakkyawar mu’amala tsakanin shugabannin siyasa, addini da al’umma.

Wannan amincewa da Tinubu ta zo ne sa’o’i kaɗan bayan jam’iyyar APC ta fitar da jerin sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *