Jam’iyyar YPP ta yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta tsawaita wa’adin Ci gaba da Rajistar Masu Kada Kuri’a (CVR), tana gargadin cewa ‘yan Najeriya da suka cancanci kada kuri’a amma har yanzu ba su yi rajista ba na iya rasa damar shiga babban zaben 2027.

Jam’iyyar ta bayyana wannan bukata ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, wadda Shugaban YPP na Babban Birnin Tarayya Abuja, Abraham Adedotun, da dan takarar jam’iyyar na majalisar dattawa a FCT, Blessing Benyeogor, suka sanya wa hannu.

YPP ta ce bukatarta ta biyo bayan damuwar da ‘yan siyasa da kungiyoyin fararen hula suka nuna kan samun damar yin rajistar masu kada kuri’a da kuma bukatar tabbatar da cewa ba a bar wani dan kasa da ya cancanta a wajen tsarin zabe ba.

Ta bukaci INEC da ta yi la’akari da koke-koken ‘yan Najeriya da ba su samu damar yin rajista ba, tare da duba hanyoyin ba su wata dama ta samun shiga cikin rajistar masu kada kuri’a.

YPP ta ce tsawaita wa’adin rajistar zai taimaka wajen kara yawan ‘yan kasar da za su shiga harkar zabe tare da kara amincewar jama’a da tsarin zaben.

A baya, INEC ta tsara gudanar da aikin CVR na 2025–2026 har zuwa ranar 30 ga Agusta 2026, amma daga bisani ta sauya jadawalin, inda ta sanya wata sabuwar ranar karshe ta gudanar da aikin, sannan daga bisani ta tsawaita matakin karshe har zuwa 26 ga Yuli 2026.

A ranar 26 ga Yuli, INEC ta sanar da cewa za ta rufe aikin rajistar, tare da kira ga ‘yan Najeriya da suka cancanta amma ba su yi rajista ba da su yi amfani da sauran lokacin da ya rage.

Daga bisani, INEC ta yi watsi da yiwuwar sake tsawaita wa’adin, tana mai cewa karin jinkiri na iya kawo cikas ga shirye-shiryenta na zaben 2027.

Hukumar ta kuma bullo da tsarin rajista ta yanar gizo da mutum zai iya yi da kansa a matakin karshe, wanda ya bai wa wadanda za su fara kada kuri’a damar kammala rajistar ta hanyar intanet.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *