Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta fara gudanar da horon kwana huɗu kan dabarun bada taimakon gaggawa (BLS) ga ma’aikatan lafiya daga asibitoci bakwai na Abuja, domin inganta yadda ake ba marasa lafiya kulawar gaggawa.
Dr Adedolapo Fasawe, Sakatariyar Sashen Lafiya da Muhalli ta FCTA, ta bayyana hakan a wata sanarwa da mai taimaka mata kan harkokin yaɗa labarai, Mrs Bola Ajao, ta fitar ranar Asabar a Abuja.
- Bai kamata Najeriya ta zama filin kisan gilla ba – Obi ga Gwamnatin Tarayya
- SERAP ta bukaci INEC ta bayyana iyakokin gudummawar siyasa da kudaden kamfen
- Malaman Musulunci 500 sun amince da takarar Tinubu
Ta ce ma’aikatan lafiya daga asibitocin Asokoro, Maitama da Wuse da Gwarinpa da Kuje da Kubwa da Nyanya ne ke halartar horon, wanda manufarsa ita ce inganta ƙwarewar ma’aikatan wajen gaggauta ɗaukar mataki idan aka samu yanayin gaggawa da kuma ba da taimakon farko domin ceton rai.
Yayin da take buɗe horon, Fasawe ta ce shirin zai taimaka wajen inganta ayyukan kula da marasa lafiya cikin gaggawa a asibitocin FCT, tare da rage mace-macen da za a iya kauce musu.
A cewar Fasawe, za a faɗaɗa horon zuwa wasu asibitocin FCT, tare da samar da kayan aikin Basic Life Support da sauran abubuwan da ake buƙata domin inganta ayyukan gaggawa da kula da marasa lafiya.
A nasa bagaren, mahalarta taron za su yaɗa ilimin da suka samu ga abokan aikinsu da kuma jama’a, domin tallafa bada taimakon kulawar gaggawa.