A shekarun baya, ƙasar Laberiya, ta kasance wani waje na neman maƙoma da ‘yanci, ga baka-fatar Amurka, amma a yau, labarin ya sauya, in da ƙasar ke cigaba da karɓar baƙin da gwamnatin Amurkan ke korowa.
A kwanakin baya, jirgin farko da ke ɗauke da mutane 20 wadanda Amurka ta koro ya sauka a filin jirgin saman Roberts International Airport, da ke kusa da babban birnin kasar Monrovia.
Wannan mataki na zuwa ne sakamakon wata yarjejeniya da za ta iya kaiwa ga tura mutane har 1,200 zuwa Laberiyan, ƙasar da mutane miliyan shida ne ke zaune a cikin ta, kuma yawancin su jikokin baƙar fatar Amurka ne da suka yi hijira tare da gina ƙasar a baya.
Mahukunta a ƙasar, sun bayyana cewa mutanen da aka kawo sun fito ne daga ƙasashen Afirka da kuma yankin yammacin duniya, bisa wata yarjejeniya da gwamnatin Amurka, na tsugunar da baƙin haure zuwa wasu ƙasashen waje.
- Gobarar daji ta lalata gandun dajin Ruvubu a Burundi
-
Tsohon Shugaban Kongo Kabila ya kalubalanci takunkumin da Amurka ta sa masa a kotu
-
Dawowar Shugaba Paul Biya na Kamaru bayan kwanakin da aka shafe ana zanga-zanga
Me yasa Laberiya?
Tarihin Laberiya na da alaƙa mai ƙarfi da Amurka, tun shekaru sama da 200 da suka wuce, ‘yantattun baƙaƙen fatar Amurka, da waɗanda aka ‘yanta daga bauta suka ƙetaro teku zuwa yankin, domin ginin sabuwar rayuwa.
Sunan ƙasar kansa, na nufin “’Yanci”. Tutar ƙasar, da sunan birnin ta Monrovia, da tsarin mulkin ta sun samo asali ne daga sunan Shugaban Amurka James Monroe, da kuma Amurkan kanta.
Da yawa daga cikin ‘yan kasar, irin su tsohon ɗan majalisar ta Conmany Wesseh (), na bayyana shakku kan ko Laberiya, da ke fafutukar farfadowa daga yakin basasa kuma ke fuskantar karancin asibitoci, gidaje, da rashin aikin yi ga matasa sama da 40 za ta iya ɗaukar wannan nauyi.
Ga ‘yan asalin Amurka mazauna Laberiya irinsu Pheta Morris da Francis Dennis, suna kallon lamarin ta fuskar jin ƙai da sake ginin sabuwar damar rayuwa, ta fuskar damammaki da ba a rasa ba.
Suna ganin kamar yadda ƙofofin Liberia suka buɗe wa kakaninsu, wannan ma wata dama ce ga sabbin wadanda Amurkan ta koro su shigo domin sake gina rayuwar su da kuma damar haifar da wasu sabbin hanyoyi, da ka iya haifar da wasu damammaki da babu irin su a baya.
Duk da cewa jami’an gwamnatin Laberiya na cewa, matakin na jin ƙai ne, kuma za a buɗe wa baƙin ƙofar neman makoma, ko kuma tafiya wata ƙasar, yanzu haka wasu korarru su biyar sun ƙi sauka a filin jirgin saman kasar dake kusa da Monrovia, hakan ya sanya aka karkata akalar jirgin da suke ciki zuwa ƙasar Equatorial Guinea.
Ko wannan zai zama wata sabuwar ƙofa ta dama ko kuma ƙarin nauyi ga ƙasar Laberiyan? Wannan ita ce tambayar da ke gaban ‘yan ƙasar a halin yanzu.