Hukumar Kula da Ilimin Shari’a ta Ƙasa (Council of Legal Education – CLE) ta dakatar da ɗaliban shari’a guda biyar daga yin jarrabawar ƙarshe ta har tsawon shekaru 10 bisa samun su da aikata maguɗin jarrabawa.

Hukumar ta ɗauki wannan matakin ne a taron ta na zango na uku, da aka gudanar ta yanar gizo a ranar 13 ga Agusta, 2026, a babbar sakatariyar Makarantar Lauyoyi ta Ƙasa da ke Bwari, a birnin Abuja.

A wata sanarwa da sakatariyar hukumar kuma daraktar gudanarwa, Aderonke Osho, ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa taron ya duba tare da amincewa da rahoton kwamitin binciken maguɗin jarrabawa kan zarge-zargen da suka taso daga jarrabawar ƙarshe ta daliban da aka shirya a watan Disambar 2025.

“Bayan duba rahotannin, Hukumar ta amince da soke takardun ɗalibai biyar da aka samu da laifin maguɗi, sannan ta dakatar da su daga zama jarrabawar har tsawon shekaru goma (10),” in ji sanarwar.

Bayan haka, hukumar ta kuma amince da hukunta waɗansu ɗalibai guda biyu sakamakon laifukan da suka shafi nuna rashin da’a, sai dai sanarwar ba ta bayyana sunayen su ko jami’o’in da suka fito ba.

Misis Osho ta ƙara da cewa taron ya kuma tattauna kan tsare-tsare, dokoki, da batutuwan da suka shafi ilimin shari’a da gudanar da makarantar lauyoyin.

A watan Afrilu da ya gabata, hukumar ta bayyana cewa ɗalibai 1,067 ne suka faɗi jarrabawar ƙarshe ta shekarar 2025 cikin ɗalibai 7,602 da suka zana jarrabawar.

Jarrabawar ƙarshen dai ita ce jarrabawar da Makarantar aikin Lauya ta Ƙasa ke gudanarwa ga ɗaliban da suka kammala karatun shari’a domin ba su takardar shaidar zama lauyoyi masu zaman kansu a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *