Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun samu nasarar dakile yunkurin safarar makamai tare da ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su a wasu ayyuka daban-daban da rundunar ta gudanar a Jihar Zamfara.
A cewar sanarwar da Jami’in Yada Labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar, ayyukan sun gudana ne a ranar 23 ga Agusta, 2026.
Sanarwar ta kara da cewa yan bindigan sun tare wata mota dauke da mutane uku da ake zargi da safarar makamai a kan hanyar Kaura Namoda zuwa Shinkafi.
- ’Yan sanda sun tarwatsa maboyar ’yan bindiga a Kaduna
- Hukumar ilimin Shari’a a Najeriya ta dakatar da wasu dalibanta tsawon shekaru 10
- Gwamnatin Tarayya na shirin sauya tsarin karatun aikin noma a manyan Makarantu
Binciken ya kai ga gano bindiga ƙirar AK 103-2 guda daya da kwanson alburusai guda daya da harsasai 30, wadanda aka boye a cikin buhun gero.
Binciken farko ya nuna cewa ana shirin kai makaman ne zuwa Yar-Galadima, da ke Karamar Hukumar Maru.
Sojojin sun kama wadanda ake zargin guda uku tare da kwace makaman da sauran kayayyakin da aka samu.
A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
A wani samame na daban a ranar, dakarun sun mayar da martani cikin gaggawa bayan samun rahoton cewa wasu ‘yan ta’adda sun kai hari kan masu ababen hawa a hanyar Anka zuwa Gummi.
Dakarun sun bi sawun ‘yan ta’addan tare da musayar wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa tare da barin dukkan mutane shida da suka yi garkuwa da su.