Sarkin Ibadan, Oba Rasheed Ladoja, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya dace ya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulkin Najeriya na tsawon lokaci, sakamakon kyawawan ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ke aiwatar wa.
Oba Ladoja ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin kaddamar da aikin fadada hanyar Ibadan zuwa Ijebu a Jihar Ogun, inda Gwamna Dapo Abiodun ya wakilci Shugaba Tinubu.
Sarkin ya jaddada cewa bai kamata a dauki taron a matsayin taron jam’iyyar (APC) ko na siyasa ba, duk da yawan ambaton jam’iyyar da ake yi yayin gudanar da taron da ya hada al’umma waje guda.
“Ina jin kowa yana ambaton APC, APC. Bola Tinubu ba mutumin APC ba ne kadai, yana aiki kuma ya dace ya kasance shugaban kasa na lokaci mai tsawo,” in ji Ladoja.
Ya kara da cewa babbar manufar taron ita ce nuna godiya ga Tinubu saboda amincewa da aikin gina hanyar, wadda ya bayyana a matsayin mai muhimmanci ga tsaro da tattalin arzikin al’umar Ibadan da kewaye.
“Wannan ba taron yakin neman zaben APC ba ne. Taro ne na mika godiya ga Mista President saboda tabbatar da wannan aiki na hanya,” in ji shi.
Basaraken ya bayyana cewa, hanyar ta dade tana fuskantar matsalar masu garkuwa da mutane, sake gina ta zai taimaka wajen inganta zirga-zirga a Jihar.
Ya ce matakin da Tinubu ya dauka ya nuna damuwar sa ga halin da mutane ke ciki, saboda haka bai kamata a kalli aikin ta fuskar wata siyasa ko kuma jam’iyya kadai ba.
Duk da haka, Sarkin ya yarda cewa ayyukan shugaban kasar na iya kara wa jam’iyyar APC damar samun nasara a zabuka masu zuwa, inda ya kara da cewa sauran jam’iyyu dole ne su shawo kan masu zabe idan har suna bukatar ganin abinda suke so.