Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI (OPHK), ta ce sama da kwamandojin ƴan ta’adda, mayaƙa da masu alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci 150 ne suka miƙa wuya a cikin mako guda.

A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labaran rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, rundunar ta danganta wannan ci gaba da ayyukan soji da ake gudanarwa bisa bayanan sirri, ƙara matsin lambar soji da kuma haɗa matakan yaƙi da waɗanda ba na yaƙi ba domin raunana ƙarfin ƙungiyoyin ta’addanci tare da ƙarfafa masu son yin watsi da ta’addanci.

Rundunar ta ce ƙaruwa a yawan masu miƙa wuya na nuna cewa matsin lamba na ƙaruwa a cikin ƙungiyoyin ƴan ta’adda, musamman kan zirga-zirgarsu, hanyoyin samun kayan aiki da kuma ikon riƙe mayaƙansu a sansanoninsu.

Ta ƙara da cewa an kwato makamai da alburusai daga wasu daga cikin waɗanda suka miƙa wuya, abin da ta ce ya ƙara tabbatar da tasirin ayyukan soji da ake gudanarwa kan hanyoyin sadarwar ƴan ta’adda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *