Sabuwar manufar Chaina ta soke harajin fiton kayayyaki da ke fitowa daga kasashen Afirka ta fara haifar da ɗa mai ido, bayan da darajar kayan da Chaina ke shigowa da su daga Najeriya ya karu da kashi 81 cikin dari, kwatankwacin dala biliyan2.25 a zangon farko na shekarar 2026.
Babbar Jakadar ƙasar Chana a Najeriya, Yan Yuqing, ce ta bayyana hakan yayin taron cin abincin rana a bikin baje kolin makamashin lantarki na kasa na bana, mai taken Nigeria International New Energy and Power Industry Expo da aka gudanar a Legas.
Yuqing ta bayyana cewa, nasarar ta samu ne watanni uku kachal da fara aiwatar da sabuwar manufar.

Hada-hadar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu ta kai dala biliyan 17.4 tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2026.
A gefe guda, Chaina ta sayi kayan Najeriya na dala biliyan 2.25 a wannan shekarar, inda aka samu ƙaruwar kaso 81 cikin dari, fiye da yadda aka samu shekarar 2025.
A watannin Mayu da Yuni kaɗai, hauhawar cinikayyar ta zarce kaso 40 cikin ɗari na hadar hadar cinikayyar da ake ƙullawa a kowane wata.
A shekarar 2025, jarin da Chaina ta zuba kai tsaye a Najeriya ya kai dala miliyan 690, inda aka samu ƙaruwar kaso 103 cikin ɗari.

A ranar 1 ga watan Mayun 2026 ne Chaina ta fara aiwatar da sabon tsari kan harajin fiton kayayyaki da ke fitowa daga kasashen Afirka 53, da ke da kyakkyawar dangantakar diflomasiyya da ita, ciki har da Nijeriya.
Manufar, na ɗaya daga cikin ƙudurorin da aka cimma a taron haɗin gwiwar Chaina da Afirka mai taken (FOCAC Beijing Action Plan 2025–2027) domin karfafa tattalin arziƙin shiyyar da kuma bunƙasa shirin Chaina na bunƙasa tattalin arziki tsakanin shekarar 2026 zuwa 2030.

A cewar Jakadiya Yan Yuqing, Najeriya na taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin Chaina, a matsayin ƙasar da ta fi gudanar da ayyukan kwangilar manyan ayyuka a faɗin nahiyar Afirka.
Sannan Najeriya ce kasuwa ta biyu mafi girma da Chana ke tunƙaho da ita wajen aika kayayyakin ta a Afirka a matsayin abokiyar cinikayya.
Ana hasashen matakin na soke harajin zai ci gaba da buɗe wa ‘yan kasuwa da manoma ‘yan Najeriya damar tura kayayyakin su zuwa babbar kasuwar ta cikin sauki.