Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce tana aiwatar da umarnin Shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu na gaggauta ceto mutanen da aka sace yayin da suke ibada a Jihar Neja.

Rundunar ta ce tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da dawowar mutanen cikin aminci.

Daraktan yaɗa labaran rundunar, Manjo Janar Michael Onoja, ya bayyana hakan yayin da yake magana kan halin da aikin ke ciki.

Shugaban  ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci rundunar sojin Najeriya, ‘yan sanda, DSS da sauran hukumomin tsaro da na leken asiri, da su ƙaddamar da wani aikin haɗin gwiwa domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

Tinubu ya ce waɗand suka kai harin kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, makiyan zaman lafiya ne kuma ba za su tsira daga fuskantar hukunci ba.

Ya kuma miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mutanen da aka kashe, tare da tabbatar musu da kokarin da gwamnatin ke yi wajen dawo da waɗanda aka sace ga iyalansu.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci hafsoshin rundunonin tsaro da su riƙa ba shi rahoto akai-akai kan ci gaban aikin ke gudana har kaiwa ga nasara.

Ya ce Najeriya ba za ta bari ayyukan ta’addanci su razana ta ba, yana mai cewa gwamnati za ta kare al’ummomi da kuma rayukan ‘yan ƙasar.

Harin ya faru ne a lokaci guda yayin gudanar da sallar Juma’a a garuruwan Dekara, Kpenya, Sabon-Gida da Gidan-Zana da ke yankin ƙaramar hukumar Borgu ta Jihar Neja.

Aƙalla mutane talatin ne aka kashe, yayin da aka yi garkuwa da wasu da dama, ta hanyar tilasta musu tafiya cikin daji, lamarin da ya sa hukumomin tsaro suka fara wani gagarumin aikin ceto bisa umarnin shugaban ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *