Najeriya da Thailand sun bayyana aniyarsu ta zurfafa haɗin gwiwar tattalin arziki, tare da ƙara bunƙasa harkokin kasuwanci da zuba jari tsakanin ƙasashen biyu domin amfanin juna.
Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta bayyana hakan ne yayin da Najeriya da Thailand suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan haɗin gwiwar fasaha a Abuja. Ambasadar ce ta sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da mataimakin Firaministan Thailand kuma Ministan Harkokin Wajen ƙasar, Sihasak Phuangketkeow, ya sanya hannu a madadin Thailand.
Ministar ta yi maraba da shirin Thailand-Africa Initiative, tare da yin kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin Nigerian Technical Aid Corps da Thailand International Cooperation Agency. Ta ce hakan zai taimaka wajen bunƙasa kwarewar ma’aikata, musayar fasaha da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa.
Ta kuma yaba da aikin haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Thailand kan bunƙasa fasahar noma mai ɗorewa, inda ta buƙaci a faɗada aikin zuwa wasu sassan Najeriya. Ta ce akwai buƙatar ƙara haɗin gwiwa wajen binciken noma, kirkire-kirkire da amfani da sabbin fasahohi.
- Shugaban ƙasa ya bayar da umarnin ceto mutanen da aka sace a Jihar Neja
- Dandalin Adzuna ya ce gurbin aikin yi ga masu shaidar digiri ya ragu a Birtaniya.
Ambasada Odumegwu-Ojukwu ta ce Najeriya na son ɗaga dangantakarta da Thailand zuwa matakin kawancen dabarun haɗin gwiwa, inda tattalin arziki zai kasance ɗaya daga cikin muhimman ginshikansa. Ta kuma buƙaci a faɗada cinikayya fiye da ɗanyen mai, shinkafa da injinan noma, zuwa masana’antu, makamashi, fasahar sadarwa, haƙar ma’adinai da makamashi mai sabuntawa.
Ta jaddada cewa Najeriya na da babbar kasuwar masu amfani da kayayyaki da kuma damarmakin zuba jari, tana mai kira ga kamfanonin Thailand da su yi amfani da damar da ƙasar ke bayarwa. Ta kuma nemi a kafa kwamitin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu domin sa ido kan aiwatar da yarjejeniyoyi da kuma hanzarta kammala yarjejeniyoyin da suka rage, ciki har da na kare zuba jari da bunƙasa cinikayya.
Najeriya ta kuma buƙaci ƙara haɗin gwiwa tsakanin kungiyar ƙasashen Kudu maso Gabashin Asiya, ASEAN, da kungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka domin buɗe sabbin damar kasuwanci, zuba jari da ci gaba. A nasa bangaren, mataimakin Firaministan Thailand, Sihasak Phuangketkeow, ya ce kafa ƙawancen tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu zai ƙara bunƙasa zuba jari da cinikayya, tare da inganta rayuwar al’ummomin ƙasashen biyu.