Matakan tura sakamakon O’level ga JAMB “daga gida”
Mataki na farko
1.⁠ ⁠A ziyarci shafin buyresultsverificationcode.ng.
2.⁠ ⁠A shigar da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) sannan a tantance ta.
3.⁠ ⁠A zaɓi ko za a ɗora sakamakon zama ɗaya ko biyu (ma’ana jarrabawa sau daya ko sau biyu), sannan a zaɓi hukumar jarabawar.
4.⁠ ⁠A shigar da adireshin email da lambar waya.
5.⁠ ⁠A biya kuɗi ta hanyar amfani da katin ATM ko tura kuɗi daga banki.
6.⁠ ⁠A shigar da lambar jarrabawa, da shekarar jarrabawa da kuma jerin/tsarin jarrabawar.
7.⁠ ⁠A tantance sakamakon sannan a karɓi Lambar Tantancewa (wato Verification Code).

Mataki na biyu: Da zarar an samu Verification Code, a bi waɗannan matakai:
•⁠ ⁠A aika saƙon VERIFY tare da Verification Code zuwa 55019 ko 66019.
•⁠ ⁠Za a karɓi sanarwa da zarar an kammala ɗora sakamakon.
Ga ɗaliban da ke amfani da sakamakon zama biyu:
Daliban da ke amfani da sakamakon jarrabawa daga zama biyu su shiga shafin JAMB e-Facility ɗinsu, sannan:
•⁠ ⁠Su danna “2026 UTME O’Level Upload”.
•⁠ ⁠Su shigar da Verification Code ɗin da aka ba su.
•⁠ ⁠Su zaɓi darussan da ake buƙata daga cikin sakamakon da aka riga aka tantance.
•⁠ ⁠Dole ne ɗalibi ya zaɓi aƙalla darussa biyar (5), amma kada su wuce tara (9).
•⁠ ⁠Kada a zaɓi darasi guda sau biyu.
•⁠ ⁠A danna “Apply the O’Level Results.”
•⁠ ⁠Za a aiko da saƙon tabbatarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *