Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya taya Hajiya Hadiza Mohammed-Aliyu murnar naɗa ta a matsayin mace ta farko da ta zama Babbar Edita ta Kamfanin  Dillancin Labarai na Najeriya NAN.

Zulum  ya ce labarin naɗin nata ya sanya shi farin ciki, ganin cewa yanzu ita ce shugabar ƙungiyar editoci da ‘yan jaridu sama da 500 da ke aiki a ofisoshin hukumar a faɗin ƙasar da kuma yankunanta 18.

Cikin wata sanarwa da mai bashi shawara akan yaɗa labarai, Dauda Iliya, ya fitar ranar Juma’a a Maiduguri, Zulum ya bayyana Hadiza Mohammed-Aliyu, wadda ta fito daga jihar Borno, a matsayin ƙwararriyar edita mai ƙwarewa, jajircewa da sanin ya kamata.

Gwamnan, ya ce Hadiza-Aliyu ta shafe tsawon shekaru 34 tana aiki a kamfanin dillancin labarai, abin da ya nuna irin gogewa da ƙwarewar da ta samu a fannin aikin jarida.

Zulum  ya ce labarin naɗin nata ya sanya shi farin ciki, ganin cewa yanzu ita ce shugabar ƙungiyar editoci da ‘yan jaridu sama da 500 da ke aiki a ofisoshin hukumar a faɗin ƙasar da kuma yankunanta 18.

Gwamnan ya yi mata fatan samun nasara tare da ƙarfafa mata gwiwar ci gaba da kiyaye ƙa’idojin aikin jarida da suka sa kamfanin dillancin labaran ya yi shura a matsayin tushen labarai da ake dogaro da su.

Ya kuma buƙaci sabuwar Babbar Editar ta ƙara ƙarfafa rawar da hukumar ke takawa wajen yaƙi da labaran ƙarya, yaɗa bayanan da ba daidai ba, bayanan yaudara da kalaman ƙiyayya, yayin da Najeriya ke shirin shiga lokacin kamfen.

Hajiya Hadiza Mohammed-Aliyu ta karanci aikin jarida a Jami’ar Maiduguri, kuma  naɗin nata ya sa ta zama mace ta farko da ta taɓa jagorantar sashen editoci na kamfanin dillancin labarai tun bayan kafa kamfanin sama da shekaru ar’bain da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *