Ma’aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta sanar cewa wasu sojoji da ke bore a sansanin sojan sama da ke birnin Yamai sun dauki matakin cutar da abokan aikinsu ta hanyar harba makamai zuwa wasu mahimman wuraren tafiyar da madafun iko.
- Majalissar Ɗinkin Duniya na buƙatar ƙarin dala biliyan ɗaya domin yaƙi da Ebola
- Ministan harkokin wajen Saudiyya ya jaddada goyon bayan Falasɗinu
- Hukumomi a Jamus na binciken asalin kasar da wani Sauro ya fito bayan mutuwar Ma’aikatan jirgi
A sanarwar da ministan tsaron kasa Janar Salifou Mody ya saka hannu wace aka karanta a gidan talbijan RTN mallakar gwamnati ta tabbatar da cewa a na ci gaba da murkushe wannan bore sannu a hankali abin da ke nufin nan ba da jimawa ba al’amura za su daidaitu.
Sanarwar ta bukaci al’umma da su ci gaba da gudanar da harakokin yau da kullum kamar yadda aka saba.