Da dama daga cikin ma’aikatan jinya ne suka fito kan titunan birnin Nairobi na Kenya, domin nuna adawa da abin da suka ce gazawar gwamnatin kasar na magance matsalolin da suka dade suna fuskanta a wuraren aikinsu.
Babban Sakataren Kungiyar Ma’aikatan Jinya ta Kenya (KNUN), Seth Panayko, ya ce ma’aikatan sun kwashe shekaru suna fama da rashin daidaito tsakanin Hukumar Albashi da Alawus-alawus ta Kenya (SRC) da kuma Majalisar Gwamnonin Jihohin kasar.
- Shugaban Green Party a Ingila na neman kujerar Majalisa
- Norway ta kwace wani jirgin ruwan Rasha a yankin Arctic
- Yadda ƙungiyoyin fararen hula suka gudanar da gangamin goyon bayan janar Tiani
Ya ce, “Shekaru da dama, tun daga 2017 har zuwa yanzu, ana ta samun rashin jituwa tsakanin SRC, wato Hukumar Albashi da Alawus-alawus, da kuma Majalisar Gwamnoni. A yau mun zo SRC domin su bayyana mana matsayinsu, sannan mu bukace su da su bayar da takardar amincewa da yarjejeniyar mu ta gama-gari ta aiki (CBA).”
Yajin aikin ma’aikatan jinyar, wanda ya fara a karshen watan Yuli, ya haifar da damuwa game da yadda lamarin ke shafar marasa lafiya.
Shugaban kungiyar ma’aikatan jinya na kenya, Collins Otieno Ajwang, ya ce yajin aikin ya shiga rana ta 37, kuma asibitocin gwamnati a fadin kasar na fama da matsaloli sakamakon rashin ma’aikatan jinya.
Shi ma Babban Sakataren kungiyar jami’an kiwon lafiya ta Kenya, Joseph Chebii, ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakin gaggawa domin kawo karshen rikicin.